<span></span>
Wata tsohuwar malama a Jami’ar Tarayya ds ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa, Dokta Ramla Muhammad Kamal, ta shigar da ƙara a kotu, inda ta ƙalubalanci korar ta daga aiki tare da zargin jami’ar da ɓata mata suna.
A shigar da jami’ar da Magatakardarta ƙara, Dokta Ramla ta buƙaci kotu ta bayyana cewa an kore ta ba bisa ƙa’ida ba.
Ta ce ba a ba ta damar kare kanta kafin a ɗauki matakin sallamarta.
Ta kuma ce jami’ar ta wallafa sunanta a matsayin malamar da ta gudu daga aiki tun kafin ta karɓi takardar korarta, lamarin da ta ce ya ɓata mata suna.
Saboda haka, ta buƙaci kotu ta umarci jami’ar ta goge sunanta da ta wallafa, ta nemi afuwarta a bainar jama’a.
Sannan ta nemi a biya ta Naira miliyan 100 da Naira miliyan 20 a matsayin diyya.
Ta ce jimillar buƙatunta sun kai kusan Naira miliyan 320.
Dokta Ramla ta bayyana cewa jami’ar ta ba ta izinin tafiya karatun digiri na gaba a Jami’ar Universiti Putra Malaysia tare da ci gaba da biyan albashinta.
Ta ce ta kammala karatun a shekarar 2023, kuma ita da iyalanta ne suka biya kuɗin makaranta, masauki, tikitin jirgi da sauran kuɗaɗen karatu.
Ta ce bayan ta kammala karatun, mijinta ya samu aiki a Amurka.
Saboda haka ta nemi a ba ta hutun rashin aiki domin ci gaba da wani ɗaukar horo tare da neman a dakatar da sharaɗin komawa aiki har sai ta dawo Najeriya.
Sai dai ta ce jami’ar ba ta amince da buƙatarta ba.
A cewarta, jami’ar ta dakatar da albashinta daga watan Mayun 2024, ta fara binciken ladabtarwa, sannan daga bisani ta kore ta daga aiki a watan Yunin 2026 ba tare da ba ta damar kare kanta yadda ya kamata ba.
Ta kuma yi zargin cewa kafin a ba ta takardar korar aiki, an fara yaɗa labarin korarta da zargin cewa jami’ar ce ta ɗauki nauyin karatunta amma ta ƙi dawowa aiki.
Ta ce wannan lamari ya ɓata mata suna.
Sai dai jami’ar da Magatakardarta sun musanta dukkanin zarge-zargen.
Jami’ar ta ce aikin Dokta Ramla yana ƙarƙashin dokokinta da kuma yarjejeniyar hutun karatu da ta sanya wa hannu kafin tafiyarta zuwa ƙasar waje.
A cewar jami’ar, ta ci gaba da biyan Dokta Ramla albashi da alawus-alawus, amma ba ta da wani nauyin biyan kuɗin makaranta, masauki, tafiye-tafiye ko sauran buƙatun karatu.
Jami’ar ta kuma ce Dokta Ramla ta karya yarjejeniyar hutun karatu saboda ba ta dawo Najeriya ba bayan ta kammala karatunta, kuma ta ci gaba da zama a Amurka ba tare da izini ba.
Baya ga kare kanta, jami’ar ta shigar da ƙarar martani, inda ta buƙaci kotu ta umarci Dokta Ramla ta dawo mata da Naira miliyan 16.4, wanda ta ce albashi da alawus-alawus ne da aka biya ta a lokacin hutun karatu.
Haka kuma jami’ar ta musanta zargin ɓata mata suna, tana mai cewa wallafa sunan Dokta Ramla ya yi daidai da umarnin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya game da ma’aikatan da ba su dawo aiki bayan kammala hutun karatu ba.
