<span></span>
Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation HADIN KAI sun ce wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu sun musu miƙa wuya a Ƙaramar Hukumar Geidam da ke Jihar Yobe.
Muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Yulin 2026, kuma an kai mutanen zuwa Maiduguri, inda suke tsare yayin da ake yi musu tambayoyi da tattara bayanan sirri.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa mutanen sun kasance cikin manyan jagororin ƙungiyar, kuma suna da cikakken bayani kan yadda take gudanar da hare-hare, tsarin jagoranci da hanyoyin samar da kayan aiki.
Ya ce bayanan da aka samu daga gare su za su taimaka wajen gano maɓoyar sauran mayaƙan Boko Haram, tare da ƙarfafa hare-haren da sojoji ke kai wa ƙungiyar a yankin Arewa maso Gabas.
Kyaftin Goni ya ƙara da cewa miƙa wuya da kwamandojin suka yi na nuna irin tasirin matsin lambar da sojoji ke ci gaba da yi ta ƙasa da sama, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, wanda ya rage wa ƙungiyar ƙarfin kai hare-hare da gudanar da ayyukanta.
