<span></span>
Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola ya kai 2,423, yayin da 967 suka rasu sakamakon cutar.
Cikin sabbin alƙaluman da mahukunta suka fitar, an samu mutum 79 a bayan nan da suka kamu da cutar a lardunan Ituri da North Kivu, da ke gabashin ƙasar.
Hukumomin lafiya sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar, tare da sa ido kan waɗanda suka yi hulɗa da masu ɗauke da ita da kuma ƙarfafa matakan kariya a yankunan da abin ya shafa.
Ebola cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar hulɗa da jinin ko ruwan jikin wanda ya kamu da ita.
Alamominta sun haɗa da zazzabi, amai, gudawa da zubar jini, kuma tana iya yin ajalin mai ɗauke da ita idan ba a yi gaggawar ba shi kulawa ba.
