<span></span>
Dakarun Sojin Najeriya sun daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka yi yunƙurin kai wa a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno, inda suka kashe wasu ’yan ta’adda tare da da fatattakar su.
Rundunar sojin ta ce ta gano kyamara mai ɗaukar bidiyo, alburusai, kakin soja da sauran kayan yaƙi daga wajem da aka yi arangamar.
Bidiyon da aka samu a cikin kyamarar ya nuna cewa manyan kwamandojin ISWAP guda huɗu da wasu ’yan kasashen waje uku ne suka shirya kai harin.
A cewar sojojin, ’yan kasashen wajen sun haɗa da wani ɗan Falasdinu da ake zargi shi ne babban mai horas da mayaƙan ƙungiyar.
Sai kuma wani ɗan ƙasar Moroko da ake zargin likitan ƙungiyar ne, da kuma wani Balarabe wanda har yanzu ba a gano sunansa ba.
Rundunar sojin ta ce wannan ya nuna cewa ISWAP na ci gaba da samun taimako da daga ƙasashen waje.
Sojoji biyu sun samu rauni a yayin musayar wuta, kuma an kai su asibiti domin samun kulawa.
Rundunar Operation HADIN KAI ta bayyana cewa rashin nasarar harin ya zama wani babban koma baya ga ISWAP.
Ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare domin daƙile ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
