<span></span>
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa ya ƙi biyan Naira miliyan 300 da masu garkuwa da mutane suka buƙata domin sakin ’yan uwansa da suka yi garkuwa da su a shekarar 2019.
Da yake jawabi a taron LABARI DA DUMI-DUMINSA A YAU YANZU da aka gudanar a Abuja, Lawal ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ya yi imanin cewa biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa masu aikata garkuwa da mutane.
A cewarsa, duk da ƙin biyan kuɗin, masu garkuwar sun saki ’yan uwansa bayan sun shafe kusan watanni uku a hannunsu. Ya jaddada cewa, ba zai taɓa yin sulhu ko biyan kuɗin fansa ga masu laifi ba.
Gwamnan ya kuma sake jaddada buƙatar kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa Gwamnoni ba za su iya ɗaukar cikakken alhakin tsaro ba alhali ba su da ikon ba hukumomin tsaro umarni kai tsaye.
Lawal ya ƙara da cewa, gwamnatin Zamfara na kashe sama da kashi 30 cikin 100 na kuɗaɗen ayyukan tsaro a jihar, inda ta samar da motocin aiki sama da 500, motocin sulke 35 da kuma jiragen sama marasa matuƙi domin tallafa wa yaƙi da ’yan bindiga.
