<span></span>
Neymar Junior, ɗan wasa mafi shahara cikin taurarin ƙwallon ƙafa daga Brazil a zamanin nan, ya sanar da yin ritaya daga buga wasa a tawagar ƙasar, bayan Brazil ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Norway.
Norway ta doke Brazil a zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya na FIFA na 2026.
An buga wasan a birnin Meadowlands na Jihar New Jersey ta Amurka, a daren ranar Lahadi 5 ga watan Yuli, 2026.
Brazil dai ƙasa ce da ta shahara a fagen ƙwallo, kuma ita ce ta fi kowa lashe gasar inda ta ɗaga kofin har sau biyar a tarihi.
An ga ɗan wasan mai shekaru 34 ya zube a ƙasa yana kuka bayan tashi daga wasan.
Kafin abokan tawagarsa su jajanta masa, kocin Brazil Carlo Ancelotti ne, ya miƙa masa hannu don ya jajanta masa.
Neymar ne ya zura ƙwallo guda da Brazil ta ci a wasan a bugun fenareti, amma hakan bai ceto Brazil ba, inda ita kuwa Norway ta wuce matakin kwata-fainal.
A wannan fili na fara buga tamaula – Neymar
Da yake jawabi cikin jimamai bayan tashi daga wasan, Neymar ya ce: “Na yi ƙoƙari. Na yi ƙoƙari. Na fara wasa a wannan filin wasa na MetLife Stadium, kuma a nan na ƙare. Yanzu dai komai ya ƙare.”
Kalaman nasa na nuna cewa Neymar ya buga wasansa na farko a tawagar Brazil a filin wasan ranar 9 ga watan Agustan 2010, a wasan sada zumunci tsakanin Brazil da Amurka.
Neymar ya yi ritaya ne a matsayin ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Brazil, da ƙwallaye 80 a wasannin 130.
Ya fara buga wa tawagar a 2010 bayan ya soma buga ƙwallon ƙwararru tare da Santos FC a 2009.
A 2016 Neymar ya lashe lambar zinare tare da tawagar a gasar Olympics.
Ɗan wasan dai ya sha fama da ciwon ƙafa, wanda ya sa wasanni biyu kawai ya iya bugawa cikin biyar a gasar ta bana.
A matakin rukuni, minti 15 kacal ya buga a wasansu da Scotland.
Neymar ya kasance mafi kyawun ɗan wasan Brazil sama da shekaru 10, duk da yawan jinya da ya yi ta fama da ita, wanda ya taƙaita tasirinsa.
