<span>Obi da Kwankwaso</span>
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a Zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar, Peter Obi, ya amince zai yi wa’adi ɗaya kacal idan aka zaɓe shi.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a hirarsa da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Ya ce shi da Obi sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta tanadi cewa Obi zai yi mulki daga 2027 zuwa 2031, sannan ya mara wa ɗan takara daga Arewacin Najeriya baya domin ci gaba da tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin yankunan ƙasar.
Da aka tambaye shi ko yana da tabbacin Obi zai cika alƙawarin, Kwankwaso ya ce yana da cikakken yaƙini.
“Eh, na yarda zai cika. Bisa abin da na sani game da shi yanzu, ba na tunanin zai sauya ra’ayinsa idan lokacin ya yi,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma ce gwamnatin NDC za ta kasance a buɗe wajen tattaunawa da ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya domin taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Sai dai ya jaddada cewa tattaunawar ba za ta maye gurbin matakan tsaro ba, yana mai cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace kan masu aikata laifuka.
Ya ce al’ummomin da rashin tsaro ya fi shafa galibi sun san masu kai hare-hare da wuraren da suke ɓuya, don haka gwamnatinsu za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin inganta tattara bayanan sirri.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa abin da ya sa ya haɗa kai da Obi shi ne yadda suka yi tarayya a mafi yawan manufofinsu na shugabanci da bunƙasa ƙasa.
“Peter Obi ɗan siyasa ne mai muhimmanta ƙasa. Da muka kwatanta manufofinmu da nasa, sai muka ga cewa kusan duk iri ɗaya ne. Wannan ne ya sa muka ga ya dace mu yi aiki tare,” in ji shi.
