<span></span>
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Gombe ta caccaki gwamnatin jihar kan zargin bai wa wani mawaƙi ɗan asalin Jihar Kano tallafin Naira miliyan 315 da kuma filaye, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Abdulkadir Ahmad Dukku ya fitar, PDP ta bayyana damuwarta kan yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a da kuma rabon kadarorin gwamnati a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa bayanan da take da su sun nuna cewa gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 115 domin sayen motar bas ƙirar Coaster ga mawaƙin, baya ga tallafin kuɗi na Naira miliyan 200, wanda jimilla ya kai Naira miliyan 315.
PDP ta ce wannan mataki ya janyo tambayoyi daga al’umma kan abubuwan da gwamnati ta bai wa fifiko, musamman a daidai lokacin da jihar ke fuskantar ƙalubale a fannoni daban-daban.
A cewar Dukku, jihar na da yara sama da 787,619 da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa da an karkatar da irin waɗannan kuɗaɗe zuwa fannin ilimi, da an taimaka wajen dawo da dubban yara makarantun boko.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan kuɗaɗe za su iya taimakawa wajen inganta harkokin lafiya, noma, samar da ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa da kuma aiwatar da wasu ayyukan raya ƙasa da za su amfani al’ummar jihar baki ɗaya.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa gwamnatin jihar ta bai wa mawaƙin filaye guda huɗu a yankin rukunin gidaje na Shehu Abubakar District Layout.
A cewarta, rabon filayen ya ƙara tayar da hankali musamman ganin cewa a baya-bayan nan an gudanar da shirin sake fasalin filaye a yankin, wanda har aka rage girman filayen da wasu suka mallaka zuwa rabin abin da aka ba su tun farko, ba tare da an biya su diyya ba.
PDP ta ce al’ummar jihar na da haƙƙin sanin dalilan da suka sa aka ware waɗannan kuɗaɗe da kadarori, tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta yi wa jama’a cikakken bayani kan lamarin.
“Domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da adalci, muna kira ga gwamnatin Jihar Gombe da ta bayyana dalilan da suka sa aka bai wa wannan mawaƙi waɗannan kuɗaɗe da kadarorin gwamnati,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da fafutukar tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jama’a yadda ya kamata domin amfanin al’ummar jihar.
Sai dai da Aminiya ta tuntuɓi Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya ce gwamnati ba za ta mayar da martani kan abin da ya kira zarge-zargen marasa tushe daga PDP ba.
A cewarsa, jam’iyyar na ƙoƙarin jawo hankalin jama’a ne domin ci gaba da kasancewa a sahun siyasa yayin da ake tunkarar zaɓe.
“Ba mu da lokacin mayar da martani ga zarge-zargen marasa tushe. Wannan wani yunƙuri ne na jam’iyyar da ta rasa tasiri, wadda ke neman jawo hankalin jama’a yayin da ake gab da shiga lokacin zaɓe,” in ji Misilli.
