<span>Shugaban gasar ƙwallon ƙafa ta La Liga ta ƙasar Spain, Javier Tebas</span>
Shugaban gasar ƙwallon ƙafa ta La Liga ta ƙasar Sifaniya, Javier Tebas, ya zargi Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) da ɗaukar matakan da ke barazana ga makomar harkar ƙwallon ƙafa.
Tebas ya bayyana wannan damuwar ce yayin da aka fara tattaunawa kan batun yiwuwar faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64.
A wata hira da ya yi da jaridar wasanni ta Italiya La Gazzetta dello Sport, Tebas ya ce FIFA na yanke hukunci ba tare da la’akari da illar da hakan zai yi wa gasar cikin gida da sauran ɓangarorin harkar ƙwallon ƙafa ba.
Ya ce harkar ƙwallon ƙafa ba Kofin Duniya kaɗai ta ƙunsa ba, yana mai cewa gasannin cikin gida ne ke rayar da wasan tare da samar da dubban guraben ayyukan yi.
“Suna lalata harkar ƙwallon ƙafa saboda wata gasa da ba ta wuce kwanaki 40 ba, wadda kuma ƙalilan daga cikin ’yan wasa ne ke taka rawa a cikinta,” in ji Tebas.
A watan Yuni ne shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa ana tattaunawa kan yiwuwar ƙara yawan ƙasashen da za su halarci gasar cin Kofin Duniya ta 2030 zuwa 64, domin bikin cika shekara 100 da fara gasar.
Sifaniya da Portugal da Morocco ne za su ja ragamar ɗaukar nauyin gasar, yayin da Paraguay da Uruguay da Argentina za su karɓi baƙuncin wasanni guda-guda.
Tebas ya ce La Liga ta sha nuna damuwarta kan yadda ake ci gaba da cunkushe jadawalin wasanni, yana mai jaddada cewa abin da ƙwallon ƙafa ke buƙata shi ne rage yawan wasannin ƙasashe da kuma kare gasannin cikin gida.
Ya kuma yi iƙirarin cewa wa’adin Gianni Infantino a matsayin shugaban FIFA ya kamata ya zo ƙarshe, yana mai cewa tsarin tafiyar da hukumar na yanzu na cike da matsaloli.
