<span></span>
Tawagar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta koma matsayi na ɗaya a sabon jadawalin ƙasashen duniya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta fitar, bayan lashe Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Sifaniya ta karɓe wannan matsayi ne daga hannun Argentina, bayan da ta doke ta da ci 1-0 a wasan ƙarshe na gasar da aka buga ranar Lahadi.
Argentina ta sauka zuwa matsayi na biyu, yayin da Faransa ta ci gaba da zama ta uku duk da rashin nasarar da ta yi a wasan neman matsayi na uku na babbar gasar tamaular da aka kammala.
Ingila ta ci gaba da zama ta huɗu duk da ita ce ta doke Faransa da ci 6-4 a wasan neman na uku na ranar Asabar.
Brazil ta haura zuwa matsayi na biyar daga na shida, yayin da Morocco ita ma ta matsa zuwa matsayi na shida.
Portugal ta sauka ƙasa inda ta tsallake matakai biyu har zuwa matsayi na bakwai, bayan Sifaniya ta fitar da ita daga gasar tun a zagayen ’yan wasa 16.
Belgium ta haura matsayi na takwas, inda ta wuce maƙwabciyarta Netherlands, wadda ta koma matsayi na tara.
Ƙasar Mexico, wadda ta ɗauki nauyin gasar tare da Amurka da Canada, ta haura matsayi huɗu zuwa na goma, karo na farko da ta shiga cikin ƙasashe goma na farko tun watan Maris na shekarar 2022.
Ita ma Jamus ta yi ƙasa da matakai biyu zuwa matsayi na 12 bayan Paraguay ta fitar da ita daga gasar.
Switzerland ta haura matakai biyar zuwa matsayi na 14 sakamakon kai wa zagayen kwata fainal, yayin da Norway ta yi wani gagarumin tsalle daga matsayi na 31 zuwa na 19, bayan ita ma ta kai zagayen kwata fainal.
