<span></span>
Dakarun Bataliya ta 19 da ke ƙarƙashin Rundunar Brigade Garrison ta Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an rundunar tsaron sa-kai (CJTF), sun daƙile wani harin kwanton ɓauna da mayaƙan Boko Haram suka kai a kan hanyar Damboa–Bulabulin–Kumala da ke Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar 4 ga Yuli, yayin da dakarun ke gudanar da sintiri tare da rakiyar ayarin motocin fararen hula a kan hanyar.
A cewar majiyoyin, jami’an tsaron sun gano wata na’urar fashewa ta IED da aka dasa a gefen hanya, kimanin kilomita biyu kafin isa Kumala.
Bayan fashewar na’urar, mayaƙan Boko Haram sun buɗe wa ayarin motocin wuta a wani yunƙurin kai hari kan sojojin da kuma motocin fararen hula.
Rahotanni sun ce dakarun sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa, inda aka yi sa’a babu wani sojan da ya ji rauni.
Sai dai bayanai sun ce fashewar na’urar ta lalata tayoyi biyu na wata motar yaƙi mai jure harin nakiya (MRAP), inda dakarun suka gaggauta sauya tayoyin nan take, kuma suka ci gaba da tafiya cikin ayari.
Bayan tsefe hanyar tare da tabbatar da aminci, dakarun sun raka motocin fararen hula 63 zuwa Kumala, sannan suka dawo suka raka wasu motoci 71 zuwa Damboa ba tare da wata matsala ba.
Majiyoyin soji sun ce wannan nasara ta nuna muhimmancin ayyukan rakiyar jami’an tsaro wajen kare matafiya da masu ababen hawa da ke amfani da hanyar Damboa–Kumala, wadda mayaƙan Boko Haram ke yawan kai hare-hare domin kawo cikas ga zirga-zirgar fararen hula da jigilar kayayyaki.
Kazalika, dakarun sun bayar da tabbacin ci gaba da gudanar da sintiri, tsefe hanyoyi da kuma rakiyar ayarin motoci domin tabbatar da tsaron matafiya da hana ’yan ta’adda samun damar kai hare-hare a manyan hanyoyin yankin Arewa maso Gabas.
