<span></span>
Dakarun Sojojin Najeriya sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Kacalla Sani Yellow a wani artabu da suka yi da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara.
Kansilan Mazabar Magaji da ke ƙaramar hukumar, Hon. Abdulmumini Sani Amma, ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce an samu nasarar ne a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa Sani Yellow na daga cikin fitattun ’yan bindigar da suka daɗe suna addabar yankin Bagega da kewaye.
“A jiya Asabar, an yi artabu tsakanin jami’an sojoji tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron rundunar sa-kai (CJTF), inda aka yi nasarar kashe Sani Yellow tare da wasu daga cikin yaransa, sai dai har yanzu ba mu tantance adadinsu ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa marigayin na daga cikin waɗanda ake zargi da dasa bama-bamai a hanyar Bagega da kuma kai hare-hare kan matafiya.
A cewarsa, artabun ya faru ne lokacin da ’yan bindigar suka kai hari kan ma’aikatan da ke aikin titin Anka zuwa Abare, wanda Gwamnan Jihar Zamfara ya bayar da kwangilar ginawa.
“Ya zo da babura sama da 40 domin kai harin, amma jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin kuma suka kashe shi,” in ji kansilan.
Ya bayyana fatan cewa idan aka ci gaba da samun irin wannan nasara kan sauran ’yan bindigar da ke yankin, al’amuran tsaro za su inganta.
Hakazalika, ya shawarci gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kai farmaki sansanonin ’yan bindiga maimakon jiran su fito suna kai hare-hare.
“A samu a kai musu hari a maɓoyarsu maimakon jiran su fito kan hanya. Hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro,” in ji shi.
