Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba
Duk da gargadin da bangaren Sin ya maimaita sau da dama, jiragen ruwan gwamnatin Philippines guda biyu sun kutsa kai cikin ruwan tekun tsibirin Huangyan na kasar Sin ba tare da izini ba jiya Alhamis. Wannan tsokana ce a karo na biyu da Philippines ta yi cikin ’yan kwanaki nan, bayan harin da ta kai wa jami’an tsaron tekun Sin a yankin ruwan Ren’ai Jiao.
Wadannan ayyukan tsokana sun faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da taron ministocin harkokin waje na Sin da kasashen ASEAN, wanda ya nuna cewa Philippines tana yunkurin kawo cikas ga yanayin tattaunawa da hadin gwiwa bisa fakewa da batun tekun kudancin Sin.
Taron ministocin harkokin waje na Sin da ASEAN ya fitar da wata alama ta a zo a gani cewa, kasashen ASEAN suna fatan kara karfafa tuntubar Sin a bangaren manyan tsare-tsare, da zurfafa hadin gwiwa a mabambantan fannoni, da kuma cimma “ka’idojin harkokin tekun kudancin Sin” tun da wuri a wannan shekara, don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin Sin tare.
A wannan taron, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya bayyana matsayin Sin kan batun tekun kudancin Sin, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen yankin su bi “Sanarwar harkokin tekun kudancin Sin da ke tsakanin bangarori daban-daban”, su kuma kaurace wa rura wutar da kasashen waje za su kunna, da adawa da yadda wasu kasashe ke tayar da hankali kan batun tekun, don kare ikon kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin Sin da kansu.
Kasashen ASEAN suna da masaniya sosai game da makarkashiyar Philippines, da kuma mugun nufin wasu kasashe. Ba shakka Sin da kasashen ASEAN suna da hikima da karfin ci gaba da magance batun tekun kudancin Sin yadda ya kamata, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin gwiwa da abota a yankin. Kazalika, za su kara hadin gwiwa don ya zama karfin ingiza ci gaban Asiya baki daya, da kuma zama abin koyi na hadin gwiwar yankin Asiya da tekun Pasifik. Kana ya zama alamar hadin kai da dogaro da kai tsakanin kasashe masu tasowa da kuma ba da ingantaccen karfin ingiza zaman lafiya mai dorewa da wadata a duniyar dake fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice. (Amina Xu)
