<span></span>
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da faɗaɗa rundunar sojin ƙasa ta Najeriya daga rundunoni takwas zuwa 12 domin ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce shugaban ya kuma amince da ɗaukar sabbin sojoji 28,000, sayen kayan yaƙi, inganta jin daɗin dakarun da kuma sabunta kayan aikin rundunar.
A cewar sanarwar, za a kafa sabbin rundunoni a Makurdi (Runduna ta 5), da Ilorin (Runduna ta 9), sai Jalingo (Runduna ta 10) da kuma Benin (Runduna ta 83).
Sabon tsarin zai sa rundunonin sojin Najeriya su kai 12, inda kowacce za ta kula da wasu jihohi da aka ware mata.
Gwamnatin ta ce za a aiwatar da shirin a matakai biyu, inda za a kammala mataki na farko nan da watan Satumba, yayin da mataki na biyu zai ƙare a watan Disamban wannan shekarar ta 2026.
Ga yadda sabon tsarin rundunonin zai kasance:
Runduna ta 1 – Kaduna (Za ta kula da Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa)
Runduna ta 2 – Ibadan (Za ta kula da Oyo, Osun, Ekiti da Ondo)
Runduna ta 3 – Jos (Za ta kula da Filato, Bauchi da Gombe)
Runduna ta 5 – Makurdi (Sabuwar rundunar da za ta kula da Benue, Nasarawa da Kogi)
Runduna ta 6 – Fatakwal (Za ta kula da Ribas, Akwa Ibom da Kuros Riba)
Runduna ta 7 – Maiduguri (Za ta kula da Borno da Yobe)
Runduna ta 8 – Sokoto (Za ta kula da Sakkwato, Kebbi da Zamfara)
Runduna ta 9 – Ilorin (Sabuwar rundunar da za ta kula da Kwara da Neja)
Runduna ta 10 – Jalingo (Sabuwar rundunar da za ta kula da Taraba da Adamawa)
Runduna ta 81 – Legas (Za ta kula da Legas da Ogun)
Runduna ta 82 – Enugu (Za ta kula da Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi da Imo)
Runduna ta 83 – Benin (Sabuwar rundunar da za ta kula da Edo, Delta da Bayelsa)
