<span></span>
Ƙasashen Turai shida na fama da gobarar daji sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta, lamarin da ya sa hukumomi suka ƙara ƙaimi wajen kashe gobarar yayin da ake ci gaba da karɓar baƙuncin masu yawon buɗe ido.
Ƙasashen da gobarar ta fi shafa sun haɗa da Faransa, Portugal, Girka, Spain, Italiya da kuma yankin Balkan, wanda ke da yawan guraren shirya fina-finai na Turai.
A Portugal, gobarar ta ƙone fiye da hekta 12,000 na dazuka, inda jami’an kashe gobara sama da 1,200 ke aikin shawo kanta, a cewar hukumomi.
A Spain, musamman a yankin Girona da ke arewa maso gabashin ƙasar, gobarar ta lalata kusan hekta 2,200, yayin da aka umarci sama da mutane 50,000 su bar gidajensu domin tsira. Haka kuma, mahukunta sun kama wani mutum da ake zargi da haddasa gobarar.
A Girka, gobarar ta tashi ne a yankin Mandra da yammacin ranar Lahadi, inda aka tura sama da jami’an kashe gobara 150 domin dakile yaɗuwarta.
A Faransa kuma, an kwashe sama da mutane 3,000 daga yankunan kudu maso yammacin ƙasar bayan Firaminista Sébastien Lecornu ya yi gargaɗin cewa gobarar na iya haddasa mummunar ɓarna idan mazauna yankunan ba su fice ba.
Tarayyar Turai ta sanar da fara ayyukan haɗin gwiwa na kashe gobara tsakanin ƙasashe domin hana gobarar yaɗuwa zuwa maƙwabtansu, tare da ba da tallafin da ya dace ga ƙasashen da bala’in ya shafa.
