<span></span>
Wasu ’yan bindiga sun sace gawar wani tsohon Mataimakin Kwamandan Hukumar Kula da Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Augustine O. Ikwue, tare da ’yan jana’iza a garin Otukpo a Jihar Benuwai.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da yamma a kan hanyar Ochadamu zuwa Ejule, da ke Ƙaramar Hukumar Ofu a Jihar Kogi.
Lokacin da lamarin ya faru motar da ke ɗauke da gawar ta faɗa tarkon ’yan bindigar.
Marigayin, wanda jami’in FRSC ne, ya rasu a garin Osogbo, Jihar Osun, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Bayan sace mutanen, ’yan bindigar ne sun tuntuɓi iyalan mamacin tare da neman Naira miliyan 450 domin sakin waɗanda suka sace.
Kwamandan FRSC na Jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace mutane tara, ciki har da jami’an FRSC biyu.
Ya bayyana cewa daga baya ’yan bindigar sun bar gawar mamacin a yankin Ejule, inda aka gano ta aka kuma miƙa wa iyalan mamacin domin yi mata jana’iza.
A cewar Fagge, maharan sun yi amfani da wayar mamacin wajen kiran matarsa tare da neman kuɗin fansa domin sakin mutanen da suka yi awon gaba da su.
Jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda, mafarauta da ’yan sa-kai sun bazama domin ceto waɗanda aka sace tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.
Jama’a a yankin sun shiga damuwa, inda da dama suka yi Allah-wadai da sace ’yan zaman makoki tare da ɗaukar gawar mamacin.
