<span></span>
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada tabbacin ci gaba da bada kuɗin hadaya kyauta da samar da masauki kusa da harami ga mahajjatan jihar.
Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne yayin da yake karɓar rahoton aikin Hajjin shekarar 2026, wanda shugaban Hukumar Hajjin Jihar, Farfesa Yakubu Yunus ya kawo masa a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.
Daga nan Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi alƙawarin inganta ayyukan aikin Hajjin 2027, yana mai tabbatar wa Hukumar Hajjin Jihar cewar gwamnati za ta ci gaba da bada duk wani tallafin ga hukumar don ganin komai na tafiya dai-dai ba tare da samun tsaiko ba tare da ci gaba da bada hadaya kyauta ga mahajjatan jihar da kuma samar musu da masauki kusa da harami.
Gwamnan ya yaba wa Hukumar bisa nasarar gudanar da ayyukan Hajjin 2026, yana mai jaddada cewa za a yi nazari a kan rahoton don ƙarfafa nasarorin da aka samu da kuma magance kurakuran da aka gano a lokacin aikin.
“Ina matuƙar farin ciki da samun rahoton ayyukan Hajjin 2026. Za mu yi nazari a kai, mu yi cikakken bincike kan abin da ya faru a lokacin aikin, sannan mu ba da shawarwari kan yadda za a inganta shi,” in ji Zulum.
Gwamna Zulum ya jaddada muhimmancin yin aiki tare tsakanin membobi da jami’an Hukumar Hajji ta Jihar Borno, yana mai jaddada cewa ya kamata a fara shirye-shiryen aikin hajji na gaba nan take.
“Dole ne mu fara shirye-shiryen aikin Hajji na 2027 yanzu; ba mu da lokaci, ina shirye don bayar da duk wani tallafi da ake buƙata don tabbatar da cewa an gudanar da aikin Hajji na 2027 ba tare da wata matsala ba,” in ji shi.
