Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso
Yayin da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027 kara karatowa, jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwasoya kawo ziyarar aiki Jihar Kaduna inda ya gana da shugabanni da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NDC da kuma kungiyar Obidient
Wakilinmu SHEHU YAHAYA ya samu damar zantawar da Kwankwaso jim kadan bayan kammala ziyarar inda ya yi bayani kan dalilin ziyararsa Kaduna, yanzu ta tabbata cewa jam’iyyar APC ba zata iya rike Nijeriya ba duba da yadda abubuwa suka tabarbare. Ga yadda hirar ta kasance:
Ka zo Jihar Kaduna Kuma ka gana da bangarori na jam’iyar NNPP, NDC da masu tafiyar OK na Peter Obi za mu so muji menene dalilin wannan hadduwa taku a Jihar Kaduna?
Da farko ina godiya ga Allah kuma ina gode wa dukkanin jama’ar Kaduna musamman wannan sassa namu da muke aiki dasu na Kwankwasiya da ita jam’iyyar NDC wanda mun tattauna dasu kuma dama shi ne dalilin wannan zuwa domin mu gaisa .
Na dade kwarai da gaske rabon da na zo wannan jiha ta Kaduna. Yawanci, yanzu mun fi tafiya a jirgi sabanin da da yawa duk wanda zai tafi Kano ta kasa ake bi.
Alhamdulillah gashi mun biyo mun zo kuma mun ga masoya mun kuma tattauna da abokan tafiyarmu ta yadda za su yi dammara su fara aiki, su hada kan mutane a wannan jiha domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta NDC ta kaiga nasara
Kuma bayanan da na ji sun bani karfin gwiwa a kan wannan tafiya ta bangaran Kwankwasiya da obi-dient wannan abin sha’awa ne kuma muna kira ga jama’a dasu tabbatar da cewa sun ba da goyan baya musamman a yanzu maganar rijistar katin masu zabe.
Kuma nan da kwana tara ana tunanin za a gama, Don haka Ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna da magoya bayanmu dama wadanda suke ganin basa goyon bayanmu. Saboda yanzu muna da lokaci daga nan zuwa Janairu mutanen Nijeriya musamman jama’ar Jihar Kaduna za su gane cewa akwai bukatar canji kuma na alheri wanda za a dakile wannan matsalar rashin tsaron da muke fama dashi sa’annan muna taya jama’ar Birnin Gwari da sauran kananan hukumomi da suke ta fama da wannan matsala da kuma matasa, abin takaici ne da damuwa yadda al’amura suka lalace a Nijeriya ta kowane bangare musamman fannin tsaro da tattalin arziki, amma abin mamaki da damuwa sai ya zamana wadanda ke rike da madafun iko ko a jikinsu.
Babu wani abu na ci gaba guda daya da zaka iya kawo cewa gwamnatin APC ta samar a Nijeriya, a kullum tafiyar kura ake yi, an mayar da mutane bayi a kasar su ta haihuwa, kuma lokaci ya gama kurewa jam’iyyar APC ya tabbata ba za ta iya ba, saboda haka lokaci ya yi da talakawa za su yi ƙumumuwa domin kawar da ita.
Yanzu halin da ake ciki kowa yana ji ajika donn haka lokaci ne da dukkan wani talaka da duk wani mabukata za su hada kai a kawo canjin da ya kamata,
Jam’iyar NDC tana fama da rikice-rikice na shugabanci, ‘yan takara da sauransu. Shin baka ganin hakan ba zai kawo muku cikas a tafiyar ku ?
Kasan ita jam’iya idan kaga ana rigima a cikinta to an hadu ne yayin da wasu jamiyya suna can suna neman wanda za su tsayar a matsayin kansila amma babu, wasu jam’iyyun ma indan aka fadi sunansu ba’a san suba saboda yanzu muna da jam’iyyun siyasa kusan guda 20 amma idan ka kirga jam’iyyu biyar ko bakwai daga su shike nan ragowar jama’a basu san sauran ba.
Kaga jam’iyyar NDC ita ce ‘yar autansu wacce a watan Disambar bara aka yi mata ragista gashi yanzu muna watan Juli kusan rabin shekara kenan amma gashi ta kewaye ko ina a Nijeriya saboda an yi sa’a mu daga bangaranmu mun shigo da Kwankwasiya cikinta. Kuma babu wata unguwa kowani gida a Arewacin Nijeriya da zaka je ka ji babu Kwankwasiya kuma a inda babu Kwankwasiya sai kaga akwai Obi-dient wannan hadaka da muka yi muna ganin Allah ya kawota ne domin ceto wannan kasa tamu . Don haka ina kira ga mutane kowa ya ba da gudunmawa kamar yadda muke wannan fafutuka da wannan gwagwarmayar domin tabbatar da talakan kasar nan musamman nan Arewa duk da gashi irin matsalolin da muke fama da su sunata shiga kudu amma dai inda ake fama da wahalar sosai shi ne Arewa. Saboda haka muke Kira ga jama’a wadanda ba su yi rijista ba su yi. Kuma su hanzarta su yi rijista da jam’iyyar mu ta NDC da ake yi yanzu.
Ya tabbatar da jam’iyar mu itace tafi kowacce jam’iyya samun daukaka da karblbar mutane wannan abune na alkhairi Kuma muna godewa alummar kasar nan akan wannan goyan bayar da suka bamu
Dan Arewa ya so jin ace Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai tsaya takarar Shugaban Kasa kawai sai aka ji Kwankwaso zai fito takarar mataimakin shugaban kasa. Kana ganin wannan zai sanya ku samu abin da kuke bukata a zaben 2027?
Kwarai kuwa za a samu, ai kasan shi dan Adam kullum sai ka yi lissafi da nazari ka duba ya zaka bada gudummawa. Ni ba neman mukami ba ne a gaba na, babban abin da nake fata shi ne yadda za a samu sauyi a kawar da muguwar gwamnati, saboda haka matukar zan bayar da tawa gudummawa to ban damu da sai na samu mukami ba.
Lokacin da na kasa dukkanin ‘yan takarar neman shugabancin Nijeriya a faifai, sai na ga Peter Obi shi ne ya dace da irin tsarin da nake dashi na ci gaban kasa da inganta rayuwar jama’a, wannan ya sa na amince muka kulla kawance, domin kamar yadda kowa ya sani ne manufar tafiyar Kwankwasiyya shi ne mayar da wanda ba kowa ba ya zama kowa, shi ya sa a tsarinmu muka ba ‘yanyan talakawa dama, muka dauki nauyin karatun su a gida da waje wanda a yau an wayi gari sun zama wadanda al’umma suke alfahari da su, to idan har za mu iya yin haka a Kano me zai hana hakan ta faruwa a Nijeriya?
Mu tafiyar da muke ta akida ce ba tafiya muke ta kudi ba saboda inda tafiyar kudi muke mun san inda kudadden suke, gasu nan a rantosu a sayar da Man fetur a karci kudi ayi abubuwa da su babu iyaka. Amma Idan ka zaga a zahiri ba zaka gani ba, toh, inda ace kudi muke nema da sai mubi Yarima asha kida. Ma’ana muma sai mubi wannan tsarin saboda wannan ba itace a gaban mu ba, mu Allah ya rufa mana asiri kuma Allah ya ba mu dama damar da muke murna da ita.
Yadda muke ba da shugabanci ga mutanen da wadanda idan sun yi maganarma ba za a ji su ba ko ihu suka yi ba ji za a yi ba saboda haka muke godiya ga Allah da ya ba mu rai da lafiya kuma ya ba mu wannan tunani da muke wannan aiki da yake dadada mana rai duk da mun sani kowa ya sani wannan aiki ba sauki ne da shi ba. Da yawa wadanda suke amfani ‘yan kadan din baso suke a sama canji ba so suke a ci gaba da tafiya a haka. Burinsu shi ne a ci gaba da yadda ake yi wato a ci gaba da sace mutane a Zamfara da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna dama sauran jihohin Arewa gaba daya, su a wurin su haka ta yi musu daidai duk da cewa akwai yawan mutane amma ‘yan kadan sun washe komai gaba daya.
Mun gode kwarai da gaske
Nima na gode
