<span></span>
Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana damuwa kan ci gaba da yaɗuwar zazzaɓin Lassa, yayin da ta yi sanadin mutuwar mutum 221 a watanni shida na farkon shekarar nan.
Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an tabbatar da kamuwar mutum 922 da cutar zuwa ƙarshen watan Yuni, yayin da kaso 24 cikin 100 na waɗanda suka kamu suka mutu, idan aka kwatanta da kaso 18.7 cikin 100 na makamancin wannan lokaci a bara.
NCDC ta ce adadin sabbin masu kamuwa da cutar ya ƙaru a makonni uku a jere, inda aka samu mutum 13 a mako na 24, mutum 22 a mako na 25, sannan adadin ya kai 31 a mako na 26.
A cewar hukumar, cutar ta bazu zuwa jihohi 23, inda Bauchi, Ondo, Taraba, Benue da Edo suka fi yawan masu kamuwa, da kusan kashi 85 cikin 100 na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a bana.
Bayanan sun kuma nuna cewa matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da aka samu sabbin kamuwa a tsakanin ma’aikatan lafiya.
Zazzaɓin Lassa cuta ce mai haɗari da ke yaɗuwa ta hanyar abinci ko sha da suka gurɓace da fitsari ko kashin ɓerayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar, kuma tana iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, musamman a cibiyoyin lafiya idan ba a ɗauki matakan kariya yadda ya kamata ba.
