Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar, ya shiga hannun ƴan bindiga bayan wani hari da suka kai a daren jiya. Rahotanni sun ce maharan sun kuma kashe jami’an tsaro huɗu da ke tare da shugaban ƙaramar hukumar lokacin da lamarin ya faru.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu, Hon. Nura Nabature, ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawa ta wayar tarho da Jagorancin Hausa. Ya ce bayan samun rahoton harin, jami’an tsaro sun bi sahun maharan tare da fafatawa da su.
A cewarsa, jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da iyalan shugaban ƙaramar hukumar da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su. Sai dai maharan sun tsere da Hon. Nura Umar tare da wani daga cikin ‘ya’yansa.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro sun bazama cikin dazuka da sauran wuraren da ake zargin maharan suka nufa domin ceto shugaban ƙaramar hukumar da yaron da ke tare da shi. Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan ci gaban aikin ceton.
