<span></span>
Ɗalibai da malaman da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Orire da ke Jihar Oyo sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.
Mai Taimakawa Shugaban ƙasa na Musamman kan Labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka sani da Twitter a baya) Onanuga ya sanar a takaice cewa masu garkuwar sun saki mutanen suka yi garkuwa da su.
“A ƙarshe dai, ɗalibai da malaman da aka sace a Orire Jihar Oyo, masu garkuwa da mutane sun sake su,” in ji shi.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai game da sakin nasu ba, ciki har da ko an biya kuɗin fansa ko kuma yanayin da ya kai ga samun ’yancinsu ba.
