<span></span>
Malamin addinin Musulunci da ke zaune a Jihar Kaduna, Sheikh Haliru Maraya ya buƙaci jam’iyyun siyasa a jihar da su guji tsayar da ɗan takarar gwamna da mataimakinsa masu addini ɗaya a babban zaɓen shekarar 2027.
Da yake magana da manema labarai a Kaduna, Maraya ya ce kasancewar jihar tana da mabiya addinai da ƙabilu daban-daban na buƙatar tsarin shugabanci mai haɗa kowa da kowa, wanda zai nuna bambancin al’umma tare da ƙarfafa zaman lafiya.
Ya ce, tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, Kaduna ta riƙa samar da Gwamna da mataimakin gwamna daga mabambantan addinai, kuma hakan ya taimaka wajen tabbatar da adalci, haɗin kai da kuma bai wa kowa damar jin cewa yana da matsayi a cikin gwamnati.
A cewarsa, gwamnatocin tsoffin gwamnoni: Ahmed Mohammed Makarfi, Namadi Sambo da marigayi Patrick Ibrahim Yakowa da Mukhtar Ramalan Yero sun tabbatar da daidaiton addini wajen tsarin shugabancin jihar.
Ya ce, “Wannan nuna adalci ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da haɗin kai da kuma sa kowa ya ji yana da muhimmanci a jihar, har ta kai babu wani yanki ko addini da ya ji an yi masa wariya a harkokin gwamnati.”
Maraya ya ce, wannan tsarin shugabanci mai haɗa kowa a lokacin waɗannan gwamnatoci ya kuma zo da ci gaba a fannin ababen more rayuwa da samar da ayyukan jin daɗin al’umma a sassa da dama na jihar.
Malamin, wanda ya taɓa zama Mai bai wa Gwamna Shawara ta Musamman kan Harkokin Addinin Musulunci a gwamnatin marigayi Patrick Yakowa da kuma gwamnatin tsohon gwamna Ramalan Yero, ya nuna damuwarsa kan yadda aka tsayar da tikitin gwamna da mataimakinsa masu addini ɗaya a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai.
Ya ce, mutane da dama da suka yi imani da adalci da daidaito ba su goyi bayan wannan tsari ba. Ya ƙara da cewa, ya kamata jam’iyyun siyasa su koma tsarin tsayar da ’yan takarar gwamna da mataimakinsa daga addinai daban-daban.
Ya ce, “Hakan zai taimaka ƙwarai wajen haɗa kan al’umma da tabbatar da wakilci na adalci a gwamnati. Addinan Musulunci da Kiristanci duka suna da mabiya masu yawa a jihar, don haka ya kamata a gudanar da al’amura ta hanyar da za ta haɗa kowa domin tare mu samu zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.”
