<span></span>
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu jami’anta sun rasa rayukansu sannan wasu sun jikkata yayin aikin ceto ɗalibai sama da 40 da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo.
Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar, bayan sanar da nasarar ceto ɗaliban da ma’aikatan makaranta da aka sace daga makarantu uku a Ƙaramar Hukumar Oriire, inda suka shafe kusan watanni biyu a hannun masu garkuwa da su.
Aminiya ta ruwaito Fadar Gwamnatin Najeriya a ranar Jumaa tana tabbatar da cewa ɗalibai da malaman da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Orire da ke Jihar Oyo sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan kwanaki 56 a tsare.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce an gudanar da aikin ceto ne bayan tsare-tsaren da aka yi cikin sirri tare da haɗin gwiwar hukumomin leƙen asiri, ’yan sanda da kuma jami’an sa-kai.
Sai dai ta ce jami’an tsaro sun yi asara a yayin aikin, ba tare da bayyana adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.
An dai danganta sace ɗaliban da mayaƙa ’yan ta’adda, duk da cewa ba a tabbatar da ƙungiyar da ta kai harin ba.
Lamarin ya girgiza al’ummar yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin yankunan da suka fi samun zamman lafiya da kwanciyar hankali.
A makon da ya gabata ne Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun yi ƙoƙarin amfani da ɗaliban a matsayin hanyar matsa wa gwamnati lamba domin a sako wasu shugabanninsu da ke tsare.
Ya ce maharan sun kuma yi barazanar kashe waɗanda suka sace idan jami’an tsaro suka kai musu farmaki.
Sai dai rundunar sojin ta ce ayyukan da ta gudanar na fiye da wata guda sun yi nasarar tarwatsa cibiyoyin maharan a dazukan Old Oyo National Park.
Ta ƙara da cewa kamen da aka yi wa wasu da ake zargi a sassa daban-daban na ƙasar ya raunana ƙungiyar, lamarin da ya tilasta musu sakin ɗaliban da malamansu ba tare da wani sharaɗi ba.
Lamarin ya sake jawo hankali kan matsalar sace ɗalibai a Najeriya, bayan irin waɗannan hare-hare da suka faru a jihohin Kebbi da Neja a ƙarshen shekarar 2025.
