Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
Akwai dabaru na zamani da ake yin amfani da su wajen yi wa ƴaƴan itatuwa aure, wato ma’ana, ana yanko wani sashe ne na wani daga cikin ƴaƴan itatuwa, sai a dasa shi a jikin wani ƴaƴan itatuwan da ake buƙata a haɗa su yi aure.
Waɗannan dabarun, ba sai an damu wani yanko jijiyar bishiya kafin a gudanar da ita ba, akwai kuma buƙatar ma’aikatan da ke renon ƴaƴan, su san yadda ake dashen na ƴaƴan itatuwan.
A wannan sharhin, za a fahimci dabarun na zamani da ke da amfani na yin dashen na ƴaƴan itatuwan da kuma sauran wasu dabarun da ba za a iya yin amfani da su a yi dashen na ƴayan itatuwan ko kuma ta hanyar yin amfani da Irin noma ba.
Za a iya samun sa’ar yin auren na ƴaƴan itatuwan ne, idan jinsinsu ya yi daidai da juna.
Akasari, an fi yin dashen ne yayin hunturu ko kuma a lokacin bazara, haka kuma ana iya yi daga tsakanin watan Yuli da Agusta da na Satumba, ko kuma a wani lokaci na daban.
Ba a ɓata wani lokaci da kuma kashe wasu kuɗaɗe masu yawa, idan za a yi dashen.
Akwai hanyoyi da dama da ake yin amfani da su, idan za a yi dashen na ƴaƴan itatuwan.
Wasu Daga Cikin Hanyoyin Da Ake Bi Domin Yin Auren ƳaƳan Itatuwa:
Ya danganta da irin ƴaƴan itatuwan da ake son a yi dashen da su a lokacin da kuma shekarar ta hanyar yin amfani da hannu.
Kayan Da Ake Amfani Da Su Domin Dashen:
Akwai kayan da ake amfani da su da dama, domin yin dashen, inda wasu daga cikinsu suka haɗa da kamar wuƙa ko kuma amfani da hannu.
