<span></span>
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ce ta kama mutum 14 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi yayin wani samame da ta kai maɓoyar masu aikata laifuka da wuraren sayar da miyagun ƙwayoyi a Kasuwar Buduwa da ke Ƙaramar Hukumar Jakusko.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.
Ya ce kwamandan shiyyar Gashuwa ne ya jagoranci samamen tare da jami’an sassan ’yan sanda na Bade A, Bade B, Gashuwa Area Command, Garin Alkali, Yusufari da Jakusko, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar sa-kai ta Peace Group Vigilante.
A cewar sanarwar, samamen ya mayar da hankali ne kan maɓoyar masu aikata laifuka da wuraren da ake zargin ana safara da kuma shan miyagun ƙwayoyi.
Rundunar ta ce an kama mutanen ne yayin da ake zargin suna sayarwa, amfani da kuma shan miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan sa maye.
Ta ƙara da cewa an ƙwato fiye da fakiti da ledoji 300 na miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da Tramadol, Vega, tabar wiwi da sauran haramtattun ƙwayoyi.
Sanarwar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike, yayin da waɗanda ake zargin ke ba jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
SP Dungus ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya umarci kwamandojin shiyyoyi, jami’an kula da ofisoshin ’yan sanda da shugabannin rundunonin musamman da su ƙara ƙaimi wajen kai samame a maɓoyar masu aikata laifuka da sauran wuraren da ake zargin ana aikata laifuka a faɗin jihar.
Ya kuma sake jaddada manufar rundunar ta rashin lamuntar safara da shan miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa su ne ke haddasa yawaitar aikata laifukan tashin hankali da sauran munanan laifuka a cikin al’umma.
Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai a kan lokaci domin tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.
