Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Kwazon Ndi Okereke-Onyuike, wacce ta kasance tsohuwar darakta janar ce ta hukumar da ke kula da kasuwar hannun jari ta Nijeriya kuma ta samu lambobin yabo da dama a kasar nan, ciki har da na Aliko Dangote, wanda a wani lokaci shi ne shugaban majalisar kasuwar jannun jari ta Nijeriya da Oscar Onyema, kwararre a kawo sauyi a shugabancin hukumar da ke kula da kasuwar hannun jari ta Nijeriya, ba karamin aiki ba ne.
Wannan shi ne abin da Umaru Kwairanga da Temi Popoola suke yi a matsayin shugaba da babban daraktan gudanarwa na rukunin musayar hannan jari a Nijeriya.
Hukumar gudanarwa ta kasuwar hannun jari ta Nijeriya ta yi fice a duniya. Sabbin bayanai daga binciken ‘Bloomberg’ na cewa kimanta musayar hannayen jari na duniya guda 92 a wannan shekara, sun nuna cewa kasuwar hannun jari ta Najeriya ta samu riba har kashi 67 cikin 100, wanda ya zarce na Kospi na Koriya ta Kudu, wanda ya zo na biyu da ribar kashi 66 cikin 100.
Ribobin sun fi samuwa ne daga kamfanonin harkokin kudade. Amma ‘Bloomberg’ ta kuma danganta yadda kasuwar ta tashi da gyaran tattalin arziki, tsayayyen farashin mai, ingantaccen canjin kudin waje, inda naira ta kara daraja da kashi 4 cikin dari kan dala tun daga watan Janairu.
Kwairanga, wanda yake da shekaru 25 na kwarewa a aikin banki, fansho, zuba jari, da masana’antu kuma a baya ya yi aiki a matsayin mamba na majalisar musayar hannayen jari, an nada shi shugaban hukumar kala da kasuwar hannun jari ta Nijeriya a watan Oktoba, 2022.
Yana cikin hukumar gudanarwa na kamfanin siminta na Ashaka da bankin Jaiz da kamfanin ‘Tangerine APT Pensions Limited’ da kamfanin FBN Senegal Limited, sannan kuma shi ne daraktan gudanarwa na Finmal Finance Serbices da wani banki na zuba jari.
Popoola, dan kasuwa a fannin harkokin zuba jari da aka horar a Wall Street, ya yi aiki a matsayin mai kula da kadarori a Landan da ke kasar Ingila a farkon aikinsa. Haka kuma, ya yi aiki a UBA, CSL Stokebrokers, sannan daga baya ya zama shugaban kamfanin ‘Renaissance Capital’. Ya zama shugaban rukunin rukunin musayar hannan jari ta Nijeriya a Janairu, 2024.
Hukumar karkashin jagorancin Kwairanga na samun ci gaba a kasuwar hannan jari da kuma bunkasan kamfanonin a Nijeriya a nan gaba kadan.
Kamfanin Airtel Africa PLC, a halin yanzu shi ne kamfani mafi daraja a kasuwr hannan jari da ke da naira tiriliyan 21.8, kusan dala biliyan 15.77. Amma a cikin manyan kamfanoni 10 mafi daraja a Afirka a shekarar 2025, babu wani kamfanin Nijeriya da ya shiga jerin. Biyu daga cikinsu na kasar Maroko ne, sauran duk suna Afirka ta Kudu.
Akwai kamfanonin sadarwa guda uku, cibiyoyin harkokin kudade guda hudu da kamfanonin hakar ma’adinai guda biyu. Naspers, kamfani fasahar sadarwa na kafar watsa labarai mai darajar kasuwar hannun jari ta dala biliyan 40 yana kan gaba.
Duk wannan zai canza ne da jerin wasu hannayen jarin matatar man Dangote a kasuwar hannun jari, wanda zai iya sa kasuwar ta zarce sauran kasuwanni a Nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
Ribarsa da tasirin sarrafa mai na cikin gida kan ma’aunin biyan kudi na kusan dukkan kasashen Afirka ba abin muhawara ba ne. Kuma yayin da masu zuwa jari ke neman cin moriyar saka babban matatar mai na Nahiyar Afirka a kasuwar hannun jari, haka nan ma mutane da ke kula da kasuwannin za su amfana.
