<span></span>
Wasu dattawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, dattawan sun ce sun samu dalilan da suka sa suka yanke shawarar mara wa APC baya, amma sun buƙaci a ba su lokaci domin su yi cikakken bayani kan matsayarsu.
Lamarin na zuwa ne yayin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban Zaɓen 2027.
