<span></span>
Jam’iyyar ADC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa da tarukan zaɓen shugabannin jihohi da kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin David Mark ya gudanar.
A jiya Litinin ce Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya haramta wa INEC amincewa ko halartar tarukan zaɓen shugabannin jihohin da kwamitin riƙon ƙwaryar ya shirya, tare da tabbatar da ci gaba da wa’adin shugabannin jihohin da aka zaɓa tun da farko.
Sai dai da take mayar da martani, ADC ta ce ta fara shirin ɗaukaka ƙarar, tana mai cewa ba ta yarda da hukuncin ba kuma tana ganin bai dace da doka ba.
Shi ma Atiku Abubakar, ta bakin mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Phrank Shuaibu, ya ce ya umarci lauyoyinsa su garzaya Kotun Ƙoli domin neman hukunci na ƙarshe kan lamarin.
Atiku ya ce saɓanin yadda wasu ke yaɗawa, hukuncin kotun bai soke zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ADC ta gudanar domin tsayar da ’yan takararta a Zaɓen 2027 ba.
Ya ce “abin da wasu ke yaɗawa cewa hukuncin ya kawo ƙarshen takarar shugaban ƙasa ta ADC wani yunƙuri ne na yaɗa bayanan da ba su dace ba domin raunana ƴan adawa da kuma ruɗar da ’yan Najeriya.”
Atiku ya bayyana cewa hukuncin kotun ya shafi zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi ne da kuma wa’adin shugabannin kwamitocin riƙo na jihohi, ba zaɓen fidda gwani na tsayar da ’yan takara ba.
Ya kuma buƙaci magoya bayan ADC kada su karaya, inda ya ce “gwagwarmayar ceto Najeriya ba ta za ta ta’allaƙa kan hukuncin kotu guda ɗaya ba.”
