<span></span>
A ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekara ɗaya cif da rasuwar.
Wannan ne ya sanya abokan tafiyarsa a lokacin da yake raye suka shirya wani gagarumin taron tunawa da shi a Abuja babban birnin ƙasar.
- Kotu ta bayar da belin Dokta Bashir Kurfi
- Matatar Dangote ta koma sayar da man fetur a farashin dalar Amurka
Buhari na daga cikin ’yan siyasa ƙalilan waɗanda suke da tarin mabiya da masoya a lokacin rayuwarsa, lamarin da ya sanya ya riƙa samun ɗimbin ƙuri’u a duk lokacin da ya yi takara, tun yana faɗuwa, har zuwa lokacin da ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.
A ranar 13 ga watan Yulin 2025 ne tsohon shugaban ƙasar ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan, shekara biyu bayan sauka daga mulki.
A taron da aka shirya na tunawa da rasuwar tasa a Abuja, babban birnin Najeriya iyalai da abokai sun taru inda suka riƙa faɗin abubuwan da suka sani game marigayin.
r
