<span></span>
Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta bayyana damuwa kan ƙarancin rijistar haihuwa da mutuwa a Najeriya, tana mai cewa har yanzu mutane da dama ba sa yin rajistar waɗannan muhimman abubuwa duk da irin muhimmancinsu ga mutum, iyali da kuma ci gaban ƙasa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a Kaduna yayin taron manema labarai da aka shirya domin sanar da fara amfani da tsarin Rijistar Haihuwa da Mutuwa na Zamani (Rijista Farar Hulɗar Lantarki da Ƙididdiga Masu Mahimmanci – E-CRVS) a faɗin ƙasar.
Shugaban Hukumar NPC, Dakta Aminu Yusuf ta bakin Kwamishinar Tarayya mai wakiltar Jihar Kaduna, Hajiya Sa’adatu Garba Dogon Bauchi, ya ce rijistar haihuwa a Najeriya ta kai kusan kashi 57 cikin 100, yayin da rajistar mutuwa ke ƙasa da kashi 20 cikin 100.
Ya ce wannan ƙarancin rijista na hana ’yan Najeriya da dama samun takardun shaidar doka, tare da rage sahihan bayanan da gwamnati ke buƙata wajen tsara manufofin kiwon lafiya, rabon albarkatu da sauran shirye-shiryen ci gaban ƙasa.
A cewarsa, rajistar haihuwa da mutuwa ba aikin ofis kaɗai ba ne, illa ginshiƙi ne na samar da ingantattun bayanan al’umma da gwamnati ke amfani da su wajen yanke hukunci da tsara ayyukan ci gaba.
Dakta Yusuf ya bayyana cewa sabon tsarin E-CRVS, wanda aka fara amfani da shi a faɗin ƙasar, zai taimaka wajen sauƙaƙa rijistar haihuwa da mutuwa ta hanyar amfani da fasahar zamani, tare da tabbatar da inganci, tsaro da sauƙin samun bayanai.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta kafa cibiyoyin rijista 4,011 a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar, tare da shirin ƙara yawan cibiyoyin domin kusantar da ayyukan ga jama’a.
Shugaban Hukumar ya yi kira ga iyaye, iyalai da cibiyoyin lafiya da shugabannin gargajiya da na addini, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su ba da haɗin kai wajen tabbatar da cewa, ana yin rajistar duk haihuwa da mutuwar da ke faruwa a kan lokaci.
Ya jaddada cewa, rajistar haihuwa da sanar da mutuwa na ci gaba da kasancewa cikin tallafin gwamnati, yana mai cewa ingantacciyar rajista ita ce tubalin samar da sahihan bayanai da inganta shugabanci da ci gaban ƙasa.
