<span></span>
Hukumomin ƙasar China sun amince da wasu sabbin dokoki da ke da nufin ƙarfafa makarantun Alƙur’ani da kuma bunƙasa ilimin addinin Musulunci a faɗin ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wani saƙo da shafin China Times ya wallafa a dandalin X.
An ce sabbin dokokin sun tanadi hanyoyin da za a inganta tsarin gudanar da makarantun addini, daidaita tsarin koyarwa da kuma ƙarfafa horar da malamai, tare da tabbatar da cewa ayyukan makarantun sun gudana bisa ƙa’idojin doka.
Haka kuma, dokokin sun ƙara fayyace haƙƙoƙi da alhakin cibiyoyin koyar da addinin Musulunci, tare da tsara yadda za su gudanar da ayyukansu cikin tsari.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin China ke ci gaba da sake fasalin dokokin da suka shafi harkokin addini da ilimi a ƙasar.
Jami’ai sun ce manufar dokokin ita ce samar da ingantaccen tsarin gudanar da ilimin addini tare da tabbatar da bin dokokin ƙasa a dukkan cibiyoyin koyar da addini.
