<span></span>
Dakarun rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, ta Operation Fansan Yammasun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su, sun kuma ƙwato dabbobi 56 da aka sace.
Sannan sun kama wani da ake zargi da ta’addanci yayin wasu samame daban-daban na sirri da suka kai a Jihar Katsina.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwar, Laftanar Kanar Aliyu Danja ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumma’a.
A cewarsa, dakarun rundunar “Sector 2″ sun ceto mutane taran ne yayin da suke gudanar da sintirin a Ƙaramar Hukumar Faskari.
Sanarwar ta Laftanar Kanar Danja ta ce: “Mutanen da aka ceto —mata uku, maza huɗu, da yara biyu—an bayyana cewa, ’yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su a ranar 9 ga watan Yuli, 2026, a kan hanyar Tsafe zuwa Kuchere da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.”
Ya ƙara da cewa, binciken farko ya nuna cewa mutanen sun tsere ne daga mavoyar ’yan ta’addan bayan da masu garkuwa da su ɗin suka yi barci, kafin daga bisani dakarun sojin su tare su kuma suka ceto su.
“A halin yanzu mutanen da aka ceton suna hannun jami’an tsaro cikin kariya, kuma suna fuskantar matakan da suka dace kafin a haɗa su da iyalansu,” in ji sanarwar.
Laftanar Kanar Aliyu Danja ya ci gaba da cewa, a wani samamen na daban, dakarun sojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri inda suka daƙile ƙoƙarin da ’yan ta’adda suka yi na sato dabbobi a Ƙaramar Hukumar Bakori.
“ ’Yan ta’addan sun buɗe wa dakarun sojin wuta, amma sun tsere zuwa cikin daji bayan da dakarun suka fi ƙarfinsu da manyan makamai.”
Aliyu Danja ya kuma bayyana cewa, dakarun sun ƙwato dabbobi 56 da aka sato waɗanda suka haɗa da shanu huɗu da tumaki 52, waɗanda a halin yanzu ake ajiye da su a sansanin soji kafin a miƙa su ga hukumomin da suka dace.
