<span></span>
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci ’yan ƙasarta da ke sassa daban-daban na duniya da su ƙara yin taka-tsantsan saboda ƙaruwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yiwuwar rikicin ya ƙara kamari.
A cikin sanarwar, ma’aikatar ta ce ’yan ƙasar su kasance cikin shiri, sannan su riƙa kula da bayanan tsaro daga hukumomi, tare da bin umarnin jami’an tsaro a ƙasashen da suke.
Sanarwar ta zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya ya ƙara faɗaɗa zuwa wasu yankuna, lamarin da ya sa ƙasashe da dama ke sa ido kan halin da ake ciki.
A bayan nan ne rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) suka sanar da kai hare-hare kan Kuwait da Jordan, inda suka ce sun kai wa cibiyar bayanan kamfanin Amazon na Amurka da ke Bahrain hari.
A gefe guda kuma, sojojin Amurka sun ce sun kammala zagaye na goma na hare-haren da suke kai wa Iran, tare da jaddada cewa zirga-zirgar jiragen ruwa za ta ci gaba da gudana a Mashigar Hormuz.
