<span>Wasu ‘yan sanda a bakin aiki</span>
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da satar wayoyin wutar lantarki, shanu, kadarorin jama’a da kuma safarar miyagun ƙwayoyi a wasu sassan jihar.
Rundunar ta ce ta ƙwato kayayyakin da suka haɗa da shanu uku, wayoyin wutar lantarki da ake zargin na sata ne, na’urar wasan PlayStation 5, talabijin guda biyu da kuma miyagun ƙwayoyi 3,427.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce an gudanar da samamen ne, bisa bayanan sirri da aka samu a Ƙananan Hukumomin Dutse, Guri, Gumel da Kazaure.
A cewar rundunar, a ranar 8 ga watan Yuli, jami’an ’yan sanda sun kama wasu matasa uku da ake zargi da lalata wayoyin lantarki da kuma karɓar kebul da ake zargin an sace a bayan wani otal a Dutse.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Aminu Mohammed mai shekara 17, Abdullahi Mustapha mai shekara 17 da Sani Umar mai shekara 18, dukkansu mazauna Dutse.
’Yan sanda sun ce kama waɗannan mutane ya taimaka wajen gano wasu da ake zargin suna karɓar kayan sata.
Rundunar ta ce: “Waɗanda ake zargin suna taimaka wa ’yan sanda wajen gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.”
A wani samame na daban, jami’an ’yan sanda sun kama Suleiman Muhammad mai shekara 23 daga Jihar Kano, bisa zargin mallakar PlayStation 5 da talabijin ƙirar plasma guda biyu da ake zargin na sata ne.
Rundunar ta ce darajar kayayyakin ta kai kusan Naira miliyan 2.5, kuma an gano masu kayan tare da miƙa musu kayayyakin.
Rundunar ’Yan Sandan Guri, tare da haɗin gwiwar ’yan banga, ta kama wani mutum da ake zargin ɓarawon shanu ne bayan gano shanu uku da ake zargin an sace an kuma ɓoye a gidansa.
Kakakin rundunar ya ce an ƙwato shanun tare da mayar wa masu su, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargin na da hannu a lamarin.
A wani samame da ’yan sanda suka kai wasu wurare da ake zargin mafakar masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Dutse, Gumel da Kazaure, an kama mutum uku.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Garba Muhammad, wanda aka fi sani da Dare, mai shekara 50; Buhari Umar, wanda aka fi sani da Uban Ƙasa, mai shekara 25; da Auwalu Dan Jos, mai shekara 25.
Rundunar ta ce ta ƙwato nau’o’in miyagun ƙwayoyi 3,427 da suka haɗa da Exol, Tramadol, Pregabalin, D5 da tabar wiwi.
Haka kuma an ƙwato kuɗi Naira 100,660 da ake zargin an samu daga cinikin miyagun ƙwayoyi.
Rundunar ta bayyana cewa za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da godiya ga al’umma bisa bayanan sirrin da suka bayarwa, waɗanda suka taimaka wajen kama waɗanda ake zargin.
Ya kuma ƙarfafa wa jama’a gwiwa su ci gaba da sanar da jami’an tsaro duk wani abin da suke zargi domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka a jihar.
