<span></span>
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta kama mutane uku da ake zargi da lalata kayayyaki da satar muhimman wayoyin wutar lantarki, tare da ƙwato wayoyin da aka sace da kayan aiki a wani gagarumin samame da ya shafi masu aikata laifuka.
Kamar yadda kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem ya ce rundunar ta yi amfani ne da wasu bayanan sirri masu inganci, jami’an rundunar ’yan sandan yankin Gashuwa sun kama mutum na farko mai suna Abubakar Idris mai shekara 27, daga yankin Sabon Gari a ranar Alhamis 23 ga Yuli, 2026.
Hukumomin sun ƙwato manyan dauri biyu na wayoyin wutar lantarki da aka sace daga waɗanda ake zargi a lokacin samamen.
Binciken ya kai ga sake kama wasu mutane biyu – Sumaila Suleiman, mai shekara 25 da Ibrahim Ado mai shekara 26.
’Yan sanda sun kuma ƙwato babur mai ƙafa uku (Keke NAPEP) mai lamba 497 DPH, wanda ake zargin ana amfani da shi wajen jigilar kayayyakin da aka sace, tare da babur ƙirar Boxer marar rijista da ake kyautata zaton an yi amfani da shi don aikata laifin.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Usman Kanfani Jibrin ya sake nanata matsayin rundunar na ci gaba da juriya wajen kama duk mutanen da ke ƙoƙarin ɓarnata kayayyakin more rayuwa na jama’a da kuma lalata tattalin arziki.
Don haka ya umurci dukkan sassan dabaru da bincike na rundunar da su ƙara himma wajen gano masu laifi da suka gudu domin tabbatar da kama su da gurfanar da su a gaban kuliya.
“Ba za mu lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga muhimman kayayyakin more rayuwa na ƙasa ba, kuma waɗanda suka aikata irin wannan laifuka za su fuskanci hukuncin da ya yi dai-dai da laifukan su,” in ji CP Jibrin.
Ana ci gaba da bincike don gano asali da kuma mallakar kayayyakin da aka ƙwato da kuma kama sauran masu laifin da ke cikin al’umma a halin yanzu.
