<span></span>
Wata Kotun Majistare da ke Jihar Katsina, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Dokta Bashir Kurfi, malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya bisa zargin ɓata sunan gwamnatin jihar.
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta gurfanar da shi a gaban kotu.
’Yan sandan sun zarge shi da yin kalaman ƙarya da kuma ɓata suna gwamnatin Jihar Katsina a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust TV a ranar 24 ga watan Yuni, 2026.
A cewar rahoton ’yan sandan, ana zargin Dokta Kurfi da cewar gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin aikin Hajjin wasu shugabannin ’yan bindiga.
’Yan sandan sun bayyana kalaman nasa a matsayin ƙarya wadda za ta iya ɓata sunan gwamnati da mutanen jihar.
An tuhume shi bisa sashe na 308 da kuma 309(1) na dokar laifuka ta Jihar Katsina.
Lokacin da aka karanta tuhumar da ake yi masa a kotu, Dokta Kurfi ya musanta zargin kuma ya ce ba shi da laifi.
Masu gabatar da ƙara sun buƙaci kotu ta ci gaba da tsare shi a hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba bincike.
Sun bayyana cewar sakin sa a wannan mataki na iya kawo cikas ga binciken.
Sai dai lauyan wanda ake tuhumar, A.D. Umar, ya roƙi kotu ta bayar da belinsa, yana mai cewa wanda yake karewa yana da damar samun ’yanci yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Alƙalin kotun, Zaharaddeen Kofar Soro, ya umarci ’yan sanda da su ci gaba da bincike, sannan ya bayar da umarnin ci gaba da tsare Dokta Kurfi har zuwa ranar da za a sake sauraron ƙarar.
An ɗage shari’ar zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Yuli, 2026.
Bayan zaman kotu, lauyan kare wanda ake tuhumar ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa za a wanke Dokta Kurfi daga zargin da ake masa.
Daga nan aka mayar da Dokta Kurfi zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) na rundunar ’yan sandan Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne bayan Dokta Kurfi ya yi zargin.
Daga baya, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta kama wasu da ake zargin shugabannin ’yan bindiga ne a lokacin da suka dawo daga aikin Hajji.
Ministan ya ce an kama su ne a filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.
