<span></span>
Babbar Kotun Jihar Borno da ke Maiduguri, ta yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari, bayan ta amsa laifin damfarar wani mutum Naira miliyan 3.5 da nufin nema masa aiki a Ƙasar Ƙatar.
Mai shari’a B.T. Zannah, ya yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2026.
Wacce ake tuhuma, mai suna Yagana Musa Mohammed, ta amsa laifin da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta shigar a kanta.
An bayyana wa kotun cewa Yagana ta karɓi kuɗin Mohammed Tukur Yaji, inda ta yi masa alƙawarin za ta sama masa da aiki a Ƙasar Ƙatar.
Sai dai ba ta cika alƙawarin da ta yi masa ba.
Lauyan EFCC, A.D. Abdulmalik, ya roƙi kotun ta yanke mata hukunci bayan ta amsa laifin.
Amma lauyanta, H.A. Aliyu, ya nemi kotun ta yi mata sassauci, inda ya bayyana cewar ta yi nadama kuma ta mayar wa wanda ta damfara kuɗinsa.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin watanni shida, ko kuma ta biya tarar Naira 50,000.
EFCC, ta ce matar ta karɓi kuɗin ne da sunan samar da aiki a ƙasashen waje, amma ba ta samar da aikin ba kuma ba ta mayar da kuɗin sai bayan da aka fara shari’ar.
Hukumar ta gargaɗin ’yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da tayin ayyukan bogi a ƙasashen waje, tare da tabbatar da sahihancin duk wani aiki kafin su bai wa kowa kuɗinsu.
