<span></span>
Fitaccen alƙalin wasan ƙwallon ƙafa na Firimiyar Ingila, Anthony Taylor, ya yi ritaya bayan shafe shekaru 16 a fagen sana’ar da aka san shi da ita.
Mashahurin ɗan jarida kuma mai sharhi kan harkokin wasan ƙwallon ƙafa, Fabrizio Romano ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
Taylor mai shekara 47 zai ajiye aikin alƙalancin ne bayan kammala Gasar Kofin Duniya, inda wasansa na ƙarshe ya kasance karawar zagayen ’yan 16 da aka fafata tsakanin Portugal da Sifaniya.
A tsawon aikinsa, Taylor ya jagoranci wasanni 831 a matakan cikin gida, Turai da na ƙasa da ƙasa.
A Ingila, ya hura wasannin ƙarshe na Gasar Kofin FA ta shekarun 2017 da 2020, da kuma na Gasar League Cup ta 2015, baya ga wasanni 432 na Gasar Firimiya.
Haka kuma, ya shafe shekara 14 cikin jerin alƙalan wasa na FIFA, inda ya wakilci Ingila a Gasar Kofin Duniya ta 2022 da ta 2026.
Da yake bayyana dalilin ritayarsa, Taylor ya ce jagorantar manyan wasanni babban abin alfahari ne, amma kuma matsin lamba da tsananin sa ido da ake yi wa alƙalan wasa sun kai matakin intaha.
“Jagorantar wasa a wannan mataki babban abin alfahari ne, amma matsin lamba da sa ido ba sa ƙarewa.
“Yanzu ne lokacin da ya dace in ajiye aiki, in kuma fara sabon babi a rayuwata,” in ji shi.
A shekarar 2023, wasu magoya bayan Roma suka yi yunƙurin kai wa Taylor hari a filin jirgin saman Budapest bayan tsohon kocin ƙungiyar, Jose Mourinho, ya soki alƙalancinsa sakamakon rashin nasarar da Roma ta yi a wasan ƙarshe na Gasar Europa League da Sevilla.
A bara ce Taylor ya bayyana cewa iyalansa sun daina zuwa kallon wasannin da yake alƙalanci saboda tsananin suka da matsin lambar da ake yi wa alƙalan wasa.
