Ƙasashen Turai shida na fama da gobarar daji sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta,...
Uzairu Rajamani
Kanumfari yana cikin kayan ƙamshi da mutane da dama suka sani a gidajen Hausawa. Ana saka shi...
Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ‘yan adawa, kan bayanan da Asusun Bayar...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da aiwatar da hukuncin hana ɗan wasan gaban tawagar...
A yau Lahadi 5 ga watan nan na Yuli, dakin nune-nunen shaidun dake tabbatar da ta’asar aikata...
Ƙungiyar likitoci masu koyon aiki ta ƙasa (NARD)ta sake ba Gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu waɗanda za...
Cibiyar Kare Haƙƙin Dan Adam da Ilimantar da Jama’a (Resource Centre for Human Rights...
A wannna makon, za mu saurari ra’ayoyin masu karatunmu ne a kan shirin ƙirƙirro da ƴansanda jihohi...
Ɗan takarar kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, daga mazaɓar Kawo, Honarabul Aminu Adam,...
A lokacin zafi na bana, an samu karuwar zafi mai tsanani a kasashen nahiyar Turai, inda kuma kayayyakin Sin na magance zafi suka jawo hankalin jama’ar kasashen sosai, kamar su na’urar sanyaya wurare ta tafi da gidanka, da laima mai fesa ruwa don magance zafin rana, da fanka da ake iya daurawa a kugu da sauransu. Wata kididdiga ta nuna cewa, yawan na’urorin sanyaya iska da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen yammacin Turai ciki har da Faransa, da Netherlands, da Belgium da sauransu, a watanni biyar na farkon bana, ya ninka har sau biyu bisa na makamancin lokaci na bara. A watan Yuni, yawan na’urorin da kasar Sin ta sayar ga nahiyar Turai, sun karu da kashi 72.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. A baya, an jima sai an huda bangwayen tsoffin gine-ginen da aka yi a kasashen nahiyar Turai, idan ana son hada na’urorin samar da sanyi wanda hakan ke kara kudin da ake kashewa don sanyaya iska, baya ga bukatar bin wasu matakai da dama. Amma daga bisani kamfanonin Sin sun gano dabarar samar da na’urorin sanyaya iska na tafi da gidanka, wadanda ba sa bukatar huda bango don kafa su. Irin wadannan na’urori na bukatar minti 10 kacal wajen hada su, da ajiye su inda ake bukata. Kayayyakin laturoni na kasar Sin suna biyan bukatun jama’ar kasashen Turai a fannin magance zafin rana a tsawon lokaci ta hanyoyin rike damar da suke da ita, da ingancinsu, da kuma hanzarin kai su wuraren da ake bukata. A halin yanzu, ana fuskantar ra’ayin killace kai daga wasu bangarori, da na bayar da kariyar cinikayya, kuma kungiyar EU ta gabatar da jerin matakan kayyade ciniki tsakaninta da kasar Sin tun daga farkon shekarar nan. Amma duk da wannan yanayi, an sayar da kayayyakin laturoni na Sin na magance zafi masu tarin yawa a sassan Turai, inda yawan kudin cinikayya a tsakanin Sin da EU a fannin, cikin watanni 5 na farkon bana ya karu da kashi 10.3 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara, wanda ya shaida cewa, tushen hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Turai shi ne samun moriyar juna. Kasar Sin tana kokarin samar da sabbin gudummawarta, wajen sa kaimi ga samun ci gaba tare a sauran sassan duniya. Lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ce, kuma za ta ci gaba da samar da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya. (Zainab Zhang)
