<span></span>
Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ‘yan adawa, kan bayanan da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), ya yi cewa an kashe kusan Naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗen gwamnati ba tare da bayyana su cikin bayanan kasafin kuɗi ba.
A yayin wani taro da aka gudanar a Jihar Legas, wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke, ya ce gwamnati ta kashe kuɗaɗe da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na jimillar arziƙin ƙasa (GDP) na Najeriya ba tare da rubuta su yadda ya kamata a bayanan kuɗaɗen gwamnati ba.
Ya ce yawancin kuɗaɗen an kashe su ne a manyan ayyuka da aka gudanar ba tare da bin tsarin kasafin kuɗi na yau da kullum ba.
Ebeke, ya bayyana cewa hakan na kawo cikas ga tantance ainihin yadda aka kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma inganta gaskiya wajen tafiyar da harkokin kuɗi.
Sai dai ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar matakan yin gyara domin inganta yadda ake bayyana irin waɗannan kuɗaɗe.
Bayanin na IMF ya sa jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara sukar gwamnati mai ci.
Atiku da Obi sun nemi a yi bincike
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, inda ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnati da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su gudanar da bincike.
Shi ma Peter Obi ya ce adadin kuɗin da aka bayyana ya yi yawa kuma bai kamata a kauda ido a kai ba.
Ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauka daga mulki, yana mai cewa lamarin ya ƙara nuna matsalar rashin gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa babu wasu kuɗaɗe da ta kashe a “ɓoye” kuma duk kuɗaɗen da take kashewa suna samun amincewar doka daga Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Ministan kuɗi ya musanta zargin
Ministan Kuɗi ya bayyana cewa abin da IMF ta yi magana a kai shi ne yadda ake gabatar da bayanan kashe kuɗaɗe, ba wai zargin an kashe kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce bambancin tsarin rahoton kuɗi bai kamata a ɗauke shi a matsayin kashe kuɗi ba bisa doka ba.
Masanin tattalin arziƙi, Marcel Okeke, ya buƙaci gwamnati da IMF su daidaita alƙaluman da wajensu, inda ya yi gargaɗin cewar lamarin na iya ɓata sunan Najeriya a idon masu zuba jari.
Ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara bayyana gaskiya domin kawar da shakku a zukatan jama’a.
