<span></span>
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shaidu a shari’ar da ake yi wa Umar Auwalu, Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu kan kisan Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci.
Yayin da yake kare kansa a kotu, Umar Auwalu mai shekara 23 ya shaida cewa shi kaɗai ne ya aikata laifin kisan kanwar babansa, Fatima Abubakar, da ‘ya’yanta shida a watan Janairu.
Ya ce wani boka kuma mai sayar da maganin gargajiya mai suna Thomas ne, ya ba shi wani turare tare da umartarsa ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka kamar yadda ya taɓa yi a baya.
Umar, ya kuma ce Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu ba su da hannu a lamarin.
A cewarsa, ya ambaci sunayensu ne bayan azabar da ya ce ya sha a hannun ’yan sanda bayan kama shi.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata, sun gabatar da jami’in ɗan sanda mai bincike, Kofural Aliyu Jamilu.
Ɓangaren masu kare waɗanda ake tuhuma ma sun gabatar da shaidunsu.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 21 ga watan Yuli, 2026.
A ranar 17 ga watan Janairun wannan ne, aka kashe Fatima Abubakar da ‘ya’yanta shida a gidansu da ke Dorayi Ciranci.
Lamarin da ya girgiza al’ummar jihar.
Bayan binciken ‘yan sanda, an kama Umar Auwalu, wanda ɗan uwa ne ga marigayiyar ne, tare da wasu mutum biyu.
An fara gurfanar da su a Kotun Majistare mai lamba 2 da ke unguwar Nomansland a ranar 5 ga watan Fabrairu kan tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai, fashi da makami da fyaɗe.
Daga bisani, bayan nazarin da Daraktan Hukumar Gurfanar da Masu Laifi (DPP) ya yi, an mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotu inda aka sake gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda tara.
Yayin da Umar ya amince da wasu zarge-zargen, sauran mutum biyu da ake tuhuma sun musanta aikata laifin.
