<span></span>
Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) sun kuɓutar da Farfesa Samuel Okunsebor, shugaban Tsangayar Noma ta Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, bayan an yi garkuwa da shi.
An sace Farfesa Okunsebor ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare a ranar Laraba a yankin Mile Uku da ke kan iyakar ƙananan hukumomin Lafia da Nasarawa Eggon.
Rahotanni sun ce jami’an DSS sun ceto shi da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Juma’a, kuma an riga an miƙa shi ga iyalansa, bayan an tabbatar da ƙoshin lafiyarsa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia.
Hukumar DSS ta kuma cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a shirya sace Farfesan, inda ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
