<span></span>
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da zargin tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, cewa ana masa barazana don hana shi shiga zaɓen 2027.
Obi, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da shirin With Chude wanda Chude Jideonwo ke jagoranta.
Ya ce yana fuskantar matsaloli da bita-da-ƙulli kuma ba shi da tabbacin kai wa lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya kuma zargi Gwamnatin Tarayya da ƙoƙarin haifar da masa da cikas a al’amuransa tare da ’yan adawa.
Bayan yaɗa kalaman na Peter Obi, lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce dalilin da ya sa fadar shugaban ƙasa ta mayar masa da martani.
A martaninsa, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ƙaryata zargin Obi.
Onanuga, ya zargi Obi da yin ƙara gishiri a wasu al’amura da kuma ƙoƙarin danganta matsalolinsa na ƙashin kansa da Gwamnatin Tarayya.
Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta fi mayar da hankali wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya kuma musanta zargin cewa gwamnatin na matsa wa bankin Fidelity Bank, inda Obi yake ds hannun jari mai tsoka a bankin.
Ya ce bankin na ci gaba da gudanar da harkokinsa cikin nasara a ƙarƙashin manufofin tattalin arziƙin gwamnati.
Fadar Shugaban Ƙasar ta ce ba ta da wata manufa ta hana Obi gudanar da harkokin siyasarsa.
Ya bayyana cewa gwamnatin za ta ci gaba da mayar da hankali kan mulki da ci gaban ƙasa maimakon rikice-rikicen siyasa.
