<span></span>
Ƙoƙarin da gwamnatoci ke yi a faɗin duniya na rage farashin man fetur ya haɗu da tsaiko, bayan farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya sake tashi sakamakon sabon rikici da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran.
Farashin ɗanyen mai, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin mai a duniya, ya kai kusan dala 79 kan kowace ganga.
Ƙasashe da dama sun fara fargabar ƙarin na iya haifar da tsadar man fetur.
Ƙarin na iya janyo ƙarin farashin man fetur da sauran kayayyaki, wanda hakan zai yi wahala gwamnatoci da ’yan kasuwa su rage farashin man a gidajen mai.
Masana harkokin makamashi sun ce tashin farashin ya samo asali ne daga rikicin Amurka da Iran, wanda hakan zai iya shafar samar da mai ko kuma hanyoyin safarar man fetur a yankin Gabas ta Tsakiya.
Gabas ta Tsakiya na daga cikin yankunan da ke samar da mafi yawan man fetur da ake amfani da shi a duniya.
Duk da matsalolin da ake fuskanta wajen haƙo mai ko manyan hanyoyin jigilar mai na iya haifar da sauyin farashi a kasuwar duniya.
A Najeriya, inda farashin man fetur ke da alaƙa da farashin ɗanyen mai a duniya da kuma canjin kuɗaɗe, masana sun ce ci gaba da tashin farashin ɗanyen mai na iya kawo cikas ga ƙoƙarin rage farashin fetur.
Wani masani kan harkokin mai da iskar gas, Dokta Marcel Okeke, ya ce mafita a wajen Najeriya ita ce ƙara adadin man da ake tacewa a cikin gida domin rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.
Ya buƙaci gwamnati ta hanzarta gyaran matatun mai na cikin gida tare da tallafa wa sabbin matatun mai domin tabbatar da wadataccen mai da rage tasirin sauye-sauyen farashin duniya.
