<span></span>
Farashin ɗanyen mai ya ƙara tashi da sama da kashi huɗu cikin ɗari a kasuwannin duniya bayan sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ke ƙara haifar da fargabar tangarɗar samar da mai.
Rikicin na zuwa ne bayan sabbin hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa juna da kuma taƙaddama kan Mashigar Hormuz, wadda Iran ta yi barazanar rufewa, yayin da Amurka ta ce mashigar a buɗe take ga jiragen ruwa.
Masana sun ce hauhawar farashin mai na iya ƙara matsa lamba ga tattalin arziƙin duniya sannan akwai yiwuwar manyan bankuna su ƙara kuɗin ruwa domin daƙile hauhawar farashi.
A kasuwannin hannayen jari kuwa, kasuwar Seoul ta faɗi da sama da kashi biyar cikin ɗari, sakamakon ci gaba da faɗuwar darajar manyan kamfanonin fasahar ƙere-ƙere musamman masu ƙera na’urorin AI.
