<span></span>
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya hana ta gudanar da ayyuka a wasu titunan Jihar Kano.
Kakakin hukumar a jihar, Abdullahi Labaran, ya ce ba su gamsu da hukuncin, kuma za su nemi kotu ta sake duba shari’ar.
Ya kuma bayyana cewa kusan kashi 90 cikin 100 na titunan Jihar Kano mallakin Gwamnatin Tarayya ne, yana mai cewa ayyukan FRSC a jihar ana gudanar da su ne a irin waɗannan tituna.
Jawabin nasa ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke kan ƙarar da lauya Abba Hikima ya shigar, inda ta hana hukumar gudanar da ayyuka a titunan da ba na Gwamnatin Tarayya ba.
