<span></span>
Gidauniyar Usman Kesoje ta tallafa wa ɗalibai 1,200 a Ƙaramar Hukumar Shagari da ke Jihar Sakkwato, da kayan karatu da suka haɗa da kayan makaranta da littattafai.
Tallafin ya amfanar da ɗalibai maza 600 da mata 600 daga makarantu 10 da ke yankin, a wani ƙoƙari na tallafa wa harkar ilimi da inganta koyo da koyarwa.
A wajen rabon kayan, mataimakin Sakataren Ilimi na Shagari, Muhammad A. Muhammad, ya yaba da tallafin, yana mai cewa ya zo a lokacin da ake buƙatarsa kuma zai taimaka wa ɗaliban.
Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyi su kwaikwayi wannan mataki domin taimakawa wajen bunƙasa ilimi a yankin.
Wakilin gidauniyar, Malam Bashiru Kesoje, ya ce Usman Abubakar Kesoje ya dukufa wajen ganin an samu ci gaban ilimi.
Ya kuma ce gidauniyar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da za su ƙarfafa yara su samu damar zuwa makaranta.
