<span></span>
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon girgizar ƙasa guda biyu da ta auku a Ƙasar Venezuela, ya kai 4,118, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.
Shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodriguez, ya ce mutum 16,740 sun jikkata sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a ranar 24 ga watan Yuni a Jihar La Guaira da ke gaɓar teku.
Girgizar ƙasar da ta auku mai ƙarfin maki 7.5, ta biyo bayan wata ta farko mai ƙarfin maki 7.2, lamarin da ya rushe gine-gine da dama tare da barin dubban mutane cikin matsala.
Duk da dakatar da aikin neman waɗanda suka tsira, wasu mutane na ci gaba da binciken baraguzan gine-gine domin neman ’yan uwansu.
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ta yi kira da a samar da kusan dala miliyan 300 domin tallafa wa ayyukan agaji da farfaɗo da yankunan da girgizar ta shafa.
Gwamnatin Venezuela ta kuma nemi a saki wasu kadarorin ƙasar da aka riƙe a ƙasashen waje domin amfani da su wajen sake gina wuraren da suka lalace.
