<span></span>
Mutum shida sun rasa rayukansu, yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.1 ta afku a yankin tsaunukan Andes na ƙasar Peru.
Firaministan ƙasar, Luis Enrique Aroyo, ya ce girgizar ta auku ne a daren Asabar a garin Chongos Bajo, mai tazarar kusan kilomita 300 gabas da babban birnin ƙasar, Lima.
Hukumar da ke kula da kare fararen hula ta ƙasar ta ce girgizar ta yi zurfin kilomita 24 cikin ƙasa, abin da ya sa ta haddasa mummunar ɓarna a yankunan da ta shafa.
Wani mazaunin garin ya shaida wa gidan talabijin na N cewa gidansu ya rushe sakamakon girgizar.
Kazalika, ya ce gidaje da dama da aka gina da tubalin laka da sauran kayan gargajiya sun rushe baki ɗaya.
Daraktan Hukumar Kare Fararen Hula ta Peru, Janar Luis Vasquez, ya ce gidaje 48 sun rushe, lamarin da ya bar mutum kusan 300 babu matsuguni ba.
Hukumar kula da girgizar ƙasa ta ƙasar ta kuma ce an sake samun ƙananan girgizar ƙasa guda 12 bayan afkuwar ta farko.
Peru na cikin yankin Pacific Ring of Fire, wanda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin yankunan da girgizar ƙasa ta fi yawaita a duniya.
Masana sun ce ƙasar na fuskantar girgizar ƙasa kusan 400 a duk shekara, sai dai galibinsu ba su da ƙarfin da mutane za su iya ji.
A shekarar 2007 ne Peru ta fuskanci ɗaya daga cikin girgizar ƙasa mafi muni a tarihinta, lokacin da wata girgiza mai ƙarfin maki 7.9 ta kashe mutum 595 a birnin Pisco da ke kudancin ƙasar, tare da haddasa ƙaramar igiyar ruwa ta tsunami.
