Ana fargabar cewa kimanin mutum huɗu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon wata mummunar guguwa mai haɗe da ruwan sama da ta afka wa wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato.
Ibtila’in wanda ya auku a ranar Asabar, ya yi ta’adi mai girman gaske ciki har da lalata gidaje, makarantar firamare da kuma asibiti.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) reshen Sakkwato ta kai ziyara yankunan da abin ya shafa domin tantance irin ɓarnar da aka yi da kuma buƙatun gaggawa na waɗanda bala’in ya shafa.
Yankunan da aka tantance sun haɗa da Mallamawa, Mai Mushe, Kaura, Sabon Gari, Rungin Tsamiya da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka.
A cewar NEMA, ɗaruruwan iyalai sun rasa matsugunansu bayan gidajensu sun rushe ko suka lalace ƙwarai, yayin da mutane da dama suka samu raunuka.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi domin isar da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, a yayin da za ta ci gaba da tantance girman asarar da bala’in ya haifar.
